Please Wait
9864
- Shiriki
Babu wani kokwanton cewa Allah (s.w.t) ya san komai, kuma a kowane hali, kuma babu wata ma’ana ga boye wa Allah wani abu, haka nan Allah (s.w.t) ba shi da hukuncin namiji ajnabi game da mace yayin addu’a? sai dai yayin ibada mutum yana samun kansa a gaban Allah madaukaki yayin da yake ganawa da shi; kuma a cikin wannan halin ya zama dole ne ya sanya tufafi mai dacewa, kuma abin da ya fi dacewa da mace shi ne hijabinta cikakke, wato; tufafin da yake nuna kamewa da tsarkin mace, kuma wannan shi ya fi dacewa da mafi kyawun lokacin halin da take ciki, wannan tufafin ne kawai ya dace da mace a yayin ibada, hatta ga maza ma, salla ba kawai tana bacewa ba ne da bayyanar da al’aura, kai ba ta dacewa da yanayin kaskan da kai da tsoron Allah da girmamawa gareshi madaukaki. Don haka bayan tufafin jiki, yana da kyau mutum ya dora wani tufafi da yake nuna mafi kololuwar girmamawa da tsarkakewa. Hada da cewa sanya lullubi yayin salla:
1. Shi sanya lullubi wani nau’i ne na kokarin sabo da kiyaye sanya lullubi a wurin da yake tilas a rayuwar yau da gobe ta kullum.
2. Yin salla a wuraren taruwar jama’a a gaban mutane da masallatai, yana bukatar sanya hijabi (lullubi) cikakke, kuma wannan lamarin yana kaiwa ga wanzuwar mace da kallonta a matsayin kamammiya a cikin al’umma, daga karshe sai mace ta iya yin sallarta da nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin wannan halin. Kuma yana da kyau mu ambaci cewa abubuwan da aka ambata a sama mun kawo su a matsayin hikimar wannan umarni na Allah, amma hadafin asali na lizimtar hijabi da sauran ibadoji shi ne tarbiyyantar da mutum bisa jin bauta ga Allah da kaskan da kai gareshi, da mika wuya ga nufi da umarnin Allah madaukaki.
Ba mu samu wani abu da yake nuni zuwa ga hikimar wannan lamarin ba a cikin ayoyi da ruwayoyi, domin asalin abin da yake janibin ibada shi ne sallama wa umarnin Allah a cikinta, kuma lizimtar umarnin mai shari’a shi ne mafi muhimmancin ma’aunin maslaha cikin lizimtar umarni da nufin mai shari’a a cikin irin wadannan mas’alolin.
Kuma duk da cewa akwai wasu maslahohin boyayyu da suke cikin wadannan lamurran da muke jahiltar su mu, sai dai an samu wasu ruwayoyi da suke nuna wasu janibobi na wasu hikimomi da maslahohin wasu hukunce-hukunen, kuma duk sa’adda ilimin dan Adam da fahimtarsa ta karu to yakan samu yayewa da bayyanar wasu daga cikin hikimomin hukuncin shari’a. kuma tabbas hijabi lullubin mace yana da nasa hikimar wurin yin salla da albarku da amfani mai yawa da ba abu ne mai gagara ba ya kasance suna da tasiri cikin wajabcinta daga Allah mahalicci. Kuma zamu yi nuni da wasu daga cikin amfanonin da wasu lamurra mustahabbai musamman game da sanya lullubi yayin salla:
1. Sanya tufafi cikakku suna kara nutsuwa ga zahirin mutum, kuma duk sa’adda tufafi suka karanta a jikin mutum to wannan yana kai wa ga karanta nutsuwa da bayyanar da karancin girman sa da rashin kula da sha’aninsa da mas’alolin rayuwar al’umma, haka nan wannan yana sanya karanta darajarsa da matsayinsa gun mutane. Don haka muna iya sanya hijabi ya zama daga cikin abubuwan ladabi na al’umma, kuma ladabi yana sanya mutum ya bayyana a gaban manya da sauran mutane da kamilallen tufafi. Yin tarayya cikin bukukuwa da tarukan addini a dukkan addinai da gurin masu hankali a duniya yana sanya mace ta sanya lullubi musamman a musulunci, ta yadda tufafin shari’a ga mace yayin halartar duk wani taro ya kasance ta sanya cikakken lullubi. A yayin da mutum yake yin salla yana fuskantar ubangiji mai daraja da daukaka mala’ikun al’arshi suna halarta yayin da yake yin wannan ibadar, kuma domin salla ta kasance tana misalta daukaka da halarta a farfajiyar Allah madaukaki, to duk sa’adda tufafin mai salla ya kasance mafi kamala da tsafta da kanshi to zai kasance ya fi a wannan halin, har ma yana daga mustahabbi ne mutane su sanya tufafin kamala yayin salla domin su kiyaye ladubba halartowa a farfajiyar Allah madaukaki da buwaya.
Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan kuwa kai ba ka ganin sa, ai shi yana ganinka” [1].
2. Daga cikin wasu fa’idojin yin lullubi yayin salla shi ne wannan aikin yana iya zama kamar wani aiki na yau da gobe da zai ci gaba don sabawa da kiyaye hijabi, kuma domin ya zama wani abu da zai taimaka wa mace ta saba da kiyaye tufafin musulunci da kiyaye shari’a ko da yaushe, da kuma kare ta daga rebacewar rashin kula da wannan lamarin. Kuma da muka ce musulunci yana kula da kiyaye lullubin mace haka nan yana kula da kiyaye ta da kare ta, kamar yadda musulunci yake kula da kamewar mace da tsarkinta, da wannan kuma zai bayyana gare mu cewa sanya lullubi ga mace yayin salla yana cikin irin wannan ne. haka nan an shardanta wa mace wannan tufafin ne domin karfafa wannan mas’alar, kuma hakika musulunci bayan cewa umarni ne da salla da wadannan sharuddan, haka nan yana koyar da wani darasin kamewa ne da suturcewa ga mace domin ya bayyanar da misali na gari na mace musulma, a lokaci guda kuma muna ganin sanya hijabi kammalalle sau biyar a rana ya fi dacewa da mace da aikin sabawa domin ta saba da hijabi lullubi cikakke.
3. Yin salla a gaban mutane a wuraren taruwa kamar masallatai da makarantu suna bukatar mace ta sanya cikakken lullubi musamman game da mata domin suturta daga ganin mutane, musamman ma cewa salla tana da ruku’u, da sujada, da tsayuwa, da zama, kuma wadannan halayen dukkansu cikakken hijabi yana kare mace daga kallon sauran mutane, domin ya kai ga kiyayewa bisa nutsuwar rai da tunanin mai salla, kuma wannan lamarin yana kai wa ga kame kai a cikin al’umma.
Kuma yana da kyau mu fadi cewa; duk abin da muka kawo wasu lamurra ne da tunaninmu yake ganewa, kuma ba dole ba ne ya kasance shi ne dalili na asasi a shari’a, domin hadafin asali a irin wadannan lamurran shi ne kaiwa ga bauta da biyayyar Allah mai girma da daukaka.
Daya daga cikin masana Allah daga malaman Iraniyawa ya yi nuni da wannan lamarin na sallamawa ga abin da ya zo daga manzon Allah (s.a.w) da wasiyyansa tsatsonsa masu tsarki da fadinsa: Mu masu mika wuya da sallamawa ne a cikin halittu, ra’ayi shi ne ra’ayin da kuke kawowa, hukunci shi ne hukuncin da kuke tabbatarwa.